Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana matsalar da ta faru a kan babbar hanyar Benin-Agbor-Asaba a matsayin wani lamari na musamman, tana mai cewa gwamnatin tarayya ta gaggauta ɗaukar mataki domin magance matsalar.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da Channels Television a ranar Laraba.
Dare ya ce bai kamata a yi amfani da matsalar wannan hanya kaɗai wajen tantance dukkan ayyukan tituna da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a faɗin ƙasar ba, domin akwai wasu hanyoyi da dama da aka kammala ko kuma ake ci gaba da aikin su ba tare da samun irin wannan matsalar ba.
Ya ce a lokacin damina, ana iya fuskantar wasu matsaloli a wuraren da ake aikin gina tituna, amma gwamnati tana da alhakin gano hanyoyin da ke buƙatar gyara tare da samar da kuɗin aikin, yayin da ‘yan kwangila ke da alhakin gudanar da aikin yadda ya kamata.
“Abin da ya faru ya nuna gazawa daga bangaren ɗan kwangilar,” in ji Dare, yana mai cewa gwamnati ta gaggauta tura manyan jami’ai da masu ruwa da tsaki zuwa wurin da matsalar ta faru domin neman mafita.
Maganar ta zo ne kwana guda bayan da Ministan Ayyuka, David Umahi, ya ziyarci hanyar Benin-Agbor-Asaba da ke Jihar Edo domin duba halin da take ciki.
Umahi ya nemi afuwar masu amfani da hanyar kan mawuyacin halin da suke fuskanta, tare da ɗaukar alhakin halin hanyar. Ya kuma soki kamfanin da ke kula da aikin tare da umartar a fara shirye-shiryen sake gina hanyar gaba ɗaya, bayan ya bayyana cewa matakan gyaran wucin-gadi ba za su wadatar ba.
Dare ya ce gaggawar da ministan, ‘yan Majalisar Dokoki da sauran masu ruwa da tsaki suka nuna wajen kai ziyara wurin matsalar na daga cikin abin da ya kira kyakkyawan shugabanci.
Ya kuma kare ayyukan gina tituna da gwamnatin Tinubu ke gudanarwa, yana mai cewa akwai buƙatar masu ababen hawa su ɗan jure wasu matsaloli yayin da ake gudanar da ayyukan gine-gine.
A cewarsa, gwamnatin tarayya na gudanar da manyan ayyukan tituna a faɗin ƙasar, ciki har da manyan tituna biyar na tarihi da kuma wasu tituna kusan 320.
Sai dai matsalar hanyar Benin-Agbor-Asaba ta jawo hankalin jama’a bayan tabarbarewar hanyar ta fara kawo cikas ga zirga-zirga, lalata motoci tare da ƙara kuɗin sufuri da kuma na gudanar da harkokin kasuwanci a yankin.
Leadership Newspapers ta ruwaito cewa Fadar Shugaban Ƙasa na kallon abin da ya faru a wannan hanyar a matsayin lamari na musamman, ba wai abin da ke wakiltar dukkan ayyukan tituna na gwamnatin tarayya ba.
