Ƙungiyar Rangers International ta Enugu ta samu nasara da ci 1-0 a kan Warri Wolves a wasan sada zumunta da aka buga ranar Asabar a filin wasa na Stephen Keshi Stadium da ke Asaba.
Wasan ya bai wa ƙungiyoyin biyu damar tantance shirinsu gabanin fara kakar 2026/27 ta Gasar Firimiya ta Najeriya (NPFL), inda masu horarwa suka gwada sabbin ‘yan wasa, suka inganta dabarun wasa da kuma ƙarfafa haɗin kan ƙungiyoyinsu.
Ga Rangers, wacce ita ce zakarar NPFL mai ci, wasan ya kasance muhimmin ɓangare na shirye-shiryenta na kare kambun gasar tare da tunkarar CAF Champions League.
A nata ɓangaren, Warri Wolves na shirin komawa babbar gasar NPFL bayan samun tikitin hawa, inda take fatan sake kafa matsayinta a cikin fitattun ƙungiyoyin ƙasar.
Mai ba Rangers shawara kan harkokin fasaha, Fidelis Ilechukwu, ta bakin mataimakinsa Odita Okechukwu, ya bayyana cewa babban abin da suka fi mayar da hankali a kai shi ne tantance sabbin ‘yan wasa da kuma ci gaba da gina ƙungiyar da za ta iya fafatawa a NPFL da CAF Champions League.
Ya ce sun gamsu da yadda ‘yan wasan suka taka rawarsu, yana mai jaddada cewa sakamakon wasan ba shi ne abin da ya fi muhimmanci ba.
Shi ma mai horar da Warri Wolves, Hassan Abdallah, ya ce wasan ya kasance mai amfani sosai wajen shirya ƙungiyarsa kafin fara sabon kakar wasa.
Ya bayyana cewa sauye-sauyen da aka yi a rabin na biyu an yi su ne domin bai wa kusan dukkan ‘yan wasan damar nuna ƙwarewarsu, tare da taimaka wa sabbin ‘yan wasa su saba da tsarin ƙungiyar.
Abdallah ya ƙara da cewa abin da ya gani a wasan ya ba shi ƙwarin gwiwa, duk da cewa har yanzu akwai wuraren da za su ci gaba da gyarawa kafin fara kakar wasa.
Ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Delta bisa ci gaba da tallafa wa Warri Wolves, yana mai fatan za a ci gaba da ba ƙungiyar goyon baya.
Duk da nasarar da Rangers ta samu, masu horar da ƙungiyoyin biyu sun amince cewa manufar wasan ta wuce sakamakon da aka samu, domin ya ba su damar gwada ƙwarewar ‘yan wasa, dabarun wasa da kuma zurfin ƙungiyoyinsu kafin fara kakar 2026/27.
