Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, , ya bayyana damuwarsa kan tsare fitaccen dan gwagwarmaya kuma mawallafi, , a gidan yarin Kuje, yana mai cewa hakan na iya zama barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya.
Obi ya yi wannan martani ne bayan wata Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Sowore har sai an saurari bukatarsa ta dakatar da aiwatar da wani umarnin kotu da ya soke belinsa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Obi ya ce yana ganin akwai bukatar a kiyaye amfani da hukumomin gwamnati wajen murkushe masu bayyana ra’ayoyi ko masu sukar gwamnati.
Ya ce dimokuraɗiyya ba ta bunƙasa ta hanyar rufe bakin masu adawa ba, sai dai ta hanyar kare ‘yancin faɗar albarkacin baki da kuma ‘yancin gudanar da tarurruka cikin lumana kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya gargadi cewa duk wani mataki da jama’a za su iya fassara a matsayin takaita ‘yancin jama’a na iya rage amincewa da hukumomin dimokuraɗiyya, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar matsalolin tsaro da kuma tsadar rayuwa.
Obi ya kuma yi kira da kada a rika kallon ‘yan gwagwarmaya, ‘yan jarida da masu sukar gwamnati a matsayin barazana ga kasa, yana mai cewa su ma suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin gwamnati.
Ya bukaci hukumomi da su ci gaba da mutunta kundin tsarin mulki da bin doka da oda wajen kare hakkokin ‘yan kasa.
A nasa bangaren, ƙungiyar kare hakkin jama’a ta SERAP ta nuna rashin jin dadinta kan tsare Sowore, tana mai cewa ana hukunta shi ne saboda amfani da hakkokinsa na kundin tsarin mulki cikin lumana.
Lamarin dai ya kara haifar da muhawara kan ‘yancin faɗar albarkacin baki, ‘yancin jama’a da kuma matsayin dimokuraɗiyya a Najeriya.
