Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta cafke wani mutum mai suna Chinedu Aniekuoku bayan an gano cewa ya kulle kuma ya daure ‘yar uwarsa, Grace Aniekuoku mai shekaru 36, da sarƙa a cikin ɗaki har tsawon shekara guda da watanni huɗu.
Kwamishinan ‘Yan Sandan FCT, Ahmed Sanusi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa a ranar 12 ga Yuni, 2026, wanda ya sanar da su cewa ana tsare da wata mata cikin mummunan hali a wani gida da ke Abuja.
Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda sun garzaya wurin amma wanda ake zargin ya hana su shiga gidan. Hakan ya sa aka yi amfani da ikon doka domin shiga gidan tare da ceto matar.
A cewar Kwamishinan, an tarar da matar cikin wani hali mai tayar da hankali, inda take rayuwa cikin najasarta ba tare da kulawa ba. Ya ce gashinta ya yi tsawo sosai, jikinta kuma ya rame ƙwarai saboda yunwa da rashin kula.
An garzaya da ita asibiti domin samun kulawar likitoci, yayin da jami’an tsaro ke fatan za ta murmure domin ta bayyana cikakken abin da ya faru.
Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya taba kwace ɗan matar kusan shekaru biyu da suka gabata zuwa wani wuri da ba a sani ba. Daga baya kuma ya kulle ‘yar uwarsa domin hana ta neman sanin inda yaron yake.
‘Yan sanda sun bayyana cewa suna ci gaba da bincike domin gano inda yaron yake tare da tabbatar da an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
