Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta fara gudanar da taron zabukan cikin gida na farko a fadin Najeriya, a wani muhimmin mataki na tsarin dimokuraɗiyyarta gabanin babban taron ƙasa na farko da aka shirya gudanarwa a ranar 9 ga Mayu, 2026 a Abuja.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam’iyyar, Abdulmumin Abdulsalam, ya fitar, inda ya bayyana fara aiwatar da shirye-shiryen a sassa daban-daban na ƙasar.
A cewar sanarwar, za a gudanar da zabukan mazabu da rumfunan zabe a ranakun 1 da 2 ga Mayu, yayin da za a yi zabukan ƙananan hukumomi a ranar 4 ga Mayu, 2026.
Wadannan matakai za su kai ga babban taron ƙasa na jam’iyyar, wanda aka tsara zai gudana a Abuja a ranar 9 ga Mayu, inda ake sa ran yanke manyan muhimman shawarwari tare da tantance tsarin shugabanci na jam’iyyar.
Abdulsalam ya bayyana cewa kwamitin shirye-shiryen taron ya kammala dukkan tsare-tsare, kuma an shirya taron gaba ɗaya. Ya ce za a gayyaci mambobin jam’iyyar da aka tantance tare da jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) domin sa ido da lura da yadda taron zai gudana kamar yadda dokar zaɓe ta tanada.
Haka kuma, an tuntuɓi hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali ga mahalarta taron, jami’ai da baƙi da za su halarta.
Shugabancin jam’iyyar ya kuma bayyana kwarin gwiwa kan jami’an jihohi da na ƙasa wajen tabbatar da cewa dukkanin zabukan cikin gida za su gudana cikin bin ƙa’idojin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya shimfiɗa.
Babban taron ƙasa na farko na NDC na ranar 9 ga Mayu, 2026, ana sa ran zai kafa ginshiƙan shugabanci da manufofin jam’iyyar na gaba.
