Tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasa, Emmanuel Babayaro, ya haɗa hannu da PAWAS Academy domin haɓaka ƙwarewar matasa ‘yan wasa a fagen ƙwallon ƙafa, tare da koyar da su dabarun kasuwanci da rayuwa.
Leadership ta rawaito cewa Babayaro, wanda tsohon mai tsaron gida ne, shi ne ɗan uwan Celestine Babayaro, wanda ya taka leda a ƙungiyoyin Chelsea da Newcastle United na Ingila, da kuma Anderlecht ta Belgium. Dukkan ‘yan uwan sun kasance cikin tawagar Najeriya da ta lashe lambar zinare a gasar Olympics ta Atlanta 1996.
An bayyana wannan haɗin gwiwa ne a lokacin Football Elite Exposure Camp (ELEX 2026) da aka gudanar a Jos, jihar Plateau, wanda daga bisani aka kammala a Abuja a ƙarshen mako.
Shirin na mako guda ya ƙunshi horo na fasaha da kuma zaman ilmantarwa na musamman da Babayaro ya jagoranta domin ƙara wa matasa fahimtar wasan ƙwallo da rayuwar bayan fili.
Daraktan PAWAS Academy, Rinji Kwarkas, ya bayyana cewa tsarin horon nasu ya dogara ne da ginshiƙai uku: wasanni, ilimi da kuma dabarun rayuwa.
Ya ce duk da cewa miliyoyin mutane suna buga ƙwallon ƙafa a duniya, kaɗan ne kawai ke samun damar zama ƙwararru, don haka ake buƙatar shirye-shiryen da ke haɗa ilimi da fasaha.
Kwarkas ya ƙara da cewa matasa ‘yan wasa su koyi fannoni daban-daban kamar tsara rayuwa, ilimin kuɗi, da kuma shirye-shiryen aiki domin rayuwa bayan wasa.
Ya kuma jaddada muhimmancin koya wa ‘yan wasa ƙarin ƙwarewa kamar ƙirar kayan wasa, dinkin riguna, rubutun wasanni da kuma nazarin wasan ƙwallo.
Babban kocin PAWAS Academy, Coach Tanko Umar, ya ce kasancewar Babayaro a shirin ya ƙara wa matasa damar samun horo daga gogaggen ɗan wasa, musamman wajen fahimtar dabarun wasa da yanke shawara a fili.
A cewarsa, an kuma raba kayan wasa ga matasan da suka halarci shirin.
Mai kula da shirin, Francis Emmanuel Tsaku, ya bayyana cewa manufarsu ita ce samar da shugabanni masu cikakken horo, ba ‘yan wasa kawai ba.
Ya ce an kammala shirin ne da wasan sada zumunta a filin wasa na Abacha Barracks da ke Abuja, wanda ya zama dama ta nuna ƙwarewar matasa a gaban masu kallon kwallon kafa da masu neman ‘yan wasa.
