Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, da Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, tare da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar APC a jihar, Sharafadeen Alli, sun bayyana alhininsu kan rasuwar fitaccen ɗan jarida kuma babban shugaban gargajiyar Ibadan, Cif Lekan Alabi.
Marigayin ya rasu ne a safiyar Asabar a birnin Legas yana da shekaru 76 a duniya.
Kafin rasuwarsa, Cif Lekan Alabi ya kasance fitaccen ɗan jarida, masani kan harkokin jama’a, jagoran al’umma, mai kare al’adun Yarbawa, kuma tsohon sakataren yaɗa labarai ga gwamnonin Jihar Oyo da dama.
A cikin sanarwar da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sulaimon Olanrewaju, ya fitar, Gwamna Makinde ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai hikima, gaskiya da sadaukar da kai wajen yi wa al’umma hidima.
Ya ce rasuwarsa babban rashi ne ga Jihar Oyo da Najeriya baki ɗaya, tare da jajanta wa iyalansa, abokansa da al’ummar Ibadan.
Shi ma Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, ya ce ya taso tare da Lekan Alabi tun suna yara a unguwar Isale-Osi da ke Ibadan, yana mai cewa marigayin ya kasance mutum mai kishin al’ada da tarihin Ibadan, kuma mutuwarsa ta girgiza shi matuƙa.
Hakazalika, ɗan takarar gwamnan APC, Sharafadeen Alli, ya bayyana Lekan Alabi a matsayin babban masani wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa a fannin aikin jarida, hidimar gwamnati da kuma harkokin masarautar gargajiya.
A nasa ɓangaren, Shugaban Central Council of Ibadan Indigenes (CCII), Cif Ajeniyi Ajewole, ya ce marigayin ya kasance gwarzon tarihi, masani kan al’adu, kuma jagora wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ɗaukaka sunan Ibadan a Najeriya da ma duniya.
Ya ƙara da cewa littattafansa, laccocinsa da ayyukansa wajen adana tarihi da al’adun Ibadan za su ci gaba da zama abin koyi ga al’ummomi masu zuwa.
