Kungiyar Save the Children International ta bayyana cewa ci gaba da hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna, abokan hulɗar ci gaba da kuma al’ummomi ne zai tabbatar da cimma burin mayar da yara 100,000 da ba sa zuwa makaranta zuwa azuzuwa a karkashin shirin Reaching Out-of-School Children (ROOSC).
Daraktan Save the Children International a Najeriya, Duncan Harvey, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna gabanin kaddamar da rahoton binciken yara marasa zuwa makaranta na jihar.
Harvey ya ce kungiyar na da kwarin gwiwar cewa idan aka ci gaba da wannan hadin gwiwa, za a samu karin yara da za su koma makaranta, su ci gaba da karatu har su kammala.
Ya bayyana cewa Save the Children na aiwatar da shirin ROOSC tare da Gwamnatin Jihar Kaduna, UNICEF, Sashen Gudanar da Aikin (PMU) da sauran abokan hulɗa, inda kowacce hukuma ke taka rawa wajen gina makarantu, horas da malamai, wayar da kan al’umma da kuma kare hakkin yara.
A cewarsa, binciken ya samar da cikakken bayani kan inda yaran da ba sa zuwa makaranta suke da kuma dalilan da ke hana su samun ilimi, lamarin da zai taimaka wajen tsara matakan da suka dace domin magance matsalar.
A nasa bangaren, Babban Masanin Kididdiga na Jihar Kaduna, Dakta Bukar Baba Alhaji, ya bayyana cewa binciken ya gano yara 187,719 da ba sa zuwa makaranta bayan da aka ziyarci gidaje 363,319 a kananan hukumomi 23 na jihar.
Ya ce Karamar Hukumar Kubau ce ta fi yawan yara marasa zuwa makaranta da adadin 25,106, sai Giwa (16,257), Makarfi (12,642), sannan Soba da Igabi da ke da 11,984 kowacce.
Dakta Alhaji ya danganta yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta da talauci, matsalar tsaro da kuma matsin tattalin arziki da ke tilasta wa yara, musamman maza, shiga noma, talla da sauran ayyukan neman abin yi maimakon zuwa makaranta.
Rahoton ya kuma nuna cewa kashi 64.6% na yaran da aka gano suna tsakanin shekaru shida zuwa 11, yayin da 60.2% ba su taba shiga makaranta ba, sannan 39.8% sun taba shiga amma daga baya suka daina.
Shi ma Daraktan Tsare-tsare na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna, Baba Lawal, ya ce an gudanar da binciken ne domin gano adadin yaran da ba sa zuwa makaranta, wuraren da suke da kuma dalilan da suka hana su zuwa makaranta, domin gwamnati ta tsara hanyoyin magance matsalar yadda ya kamata.
A nasa jawabin, Mai Kula da Shirin ROOSC, Ezra Angai, ya ce rahoton ya samar wa jihar ingantattun bayanai da za su jagoranci zuba jari da shirye-shiryen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ya bayyana cewa shirin zai gina sabbin makarantu 102, ya gyara makarantu 170, tare da kafa cibiyoyin koyarwa a fadin jihar. Ya kara da cewa a halin yanzu ana aikin gina makarantu 42, ciki har da sabbin makarantu 16, yayin da aka fara shirye-shiryen gina karin makarantu 30 da gyaran wasu makarantu 60.
Har ila yau, ya ce an samar da tsarin sa ido domin bibiyar yaran da suka koma makaranta, gano masu fuskantar barazanar daina karatu da daukar matakan da za su tabbatar da sun ci gaba da kasancewa a makaranta.
