Kakakin kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), Farfesa Tukur Mohammed-Baba, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya rasa gagarumin goyon baya a Arewacin Najeriya tun bayan zaben 2023, amma ya ce har yanzu babu wani dan siyasa da ya gabatar da ingantaccen madadi a gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Ya soki Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, yana mai cewa ba su fito da sahihan manufofi kan tattalin arziki, tsaro da sauran matsalolin da ke addabar kasar ba.
