Kotun Babbar Jihar Anambra da ke Ogidi ta yanke wa wani jagoran mawakan coci mai suna James Mary Onuorah hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari bayan samunsa da laifin yi wa wata yarinya mai shekaru 16 fyade da sunan yi mata “deliverance”.
Kotun ta bayyana cewa wanda ake tuhumar ya yaudari mahaifiyar yarinyar da cewa ‘ya’yanta na fama da aljanu da “mijin aljani”, lamarin da ya sa ta rika kai su gidansa domin yi musu addu’o’i.
Bayan shari’a mai tsawo, kotun ta tabbatar da cewa an gabatar da hujjoji masu gamsarwa, ciki har da cewa yarinyar ta samu ciki kuma ta haifi jariri sakamakon abin da ya faru.
Alkalin kotun ya yanke masa hukuncin shekara 25 saboda fyade, shekara 7 saboda wani laifin cin zarafi, kuma hukuncin zai gudana lokaci guda. Haka kuma kotun ta umarce shi da ya biya yarinyar diyyar Naira miliyan 5.
