Shugaban Hukumar Tennis ta Najeriya (NTF), Rt. Hon. Victor Ochei, ya taya ƙungiyoyin ƙwallon Tennis na maza da mata na ƙasa murnar nasarar tarihi da suka samu bayan dukkansu sun samu ɗaukaka zuwa manyan matakan gasa a duniya.
Ƙungiyar matan Najeriya ta samu tikitin hawa zuwa Billie Jean King Cup Europe/Africa Zone Group II, yayin da ƙungiyar maza ta samu ɗaukaka zuwa Davis Cup World Group II, lamarin da ya zama karo na farko da ƙungiyoyin biyu suka samu irin wannan nasara a shekara guda.
Ochei ya yabawa ‘yan wasan da masu horar da su kan jajircewa, ƙwazo da haɗin kai da suka nuna a gasar.
Ya ce wannan nasara ta nuna ci gaban da ake samu a harkar tennis ta Najeriya da kuma tasirin sabbin tsare-tsaren da hukumar ke aiwatarwa domin bunƙasa wasan.
Shugaban NTF ya kuma gode wa Hukumar Wasanni ta Ƙasa (NSC), musamman Shugabanta Malam Shehu Dikko da Darakta Janar Hon. Bukola Olopade, bisa goyon bayan da suka bayar wajen samar da yanayin da ya bai wa ‘yan wasan damar yin fice.
Ochei ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da zuba jari wajen bunƙasa tennis daga matakin ƙananan yara, gano sababbin hazikai da ƙarfafa gasa domin Najeriya ta ci gaba da yin fice a matakin ƙasa da ƙasa.
