Masu kula da harkokin fitaccen ɗan TikTok kuma mai shirya fina-finai, Joseph Prince, wanda aka fi sani da Joffy, sun musanta rahotannin da ke yawo cewa ya rasu.
A wata sanarwa da aka fitar ta shafinsa na TikTok a ranar Juma’a, masu kula da harkokinsa sun bayyana cewa Joffy yana raye kuma yana karɓar magani a asibiti bayan da aka kai masa hari, inda aka ce an caka masa wuka.
Sanarwar ta ce hotunan Joffy yana kwance a gadon asibiti da aka wallafa sun tabbatar da cewa rahotannin mutuwarsa da ke yawo a kafafen sada zumunta ba gaskiya ba ne.
A cewar sanarwar:
“Muna bayyana a fili cewa rahotannin da ke cewa Joseph Prince (Joffy) ya rasu ba gaskiya ba ne. Yana raye.”
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da Joffy da tawagar Joseph Prince Films ke dawowa daga wani gangamin tallata tikitin sabon fim ɗinsu mai suna The Last Bell, inda suke ɗaukar bidiyon ayyukansu kafin wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai musu hari.
Masu kula da harkokinsa sun buƙaci masoya da al’umma su yi watsi da jita-jitar mutuwarsa tare da ci gaba da yi masa addu’ar samun lafiya.
