Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ce ba za a samu ci gaba mai ɗorewa ba sai idan al’umma suna taka rawa kai tsaye wajen tsara da kuma sa ido kan ayyukan ci gaba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da zagaye na biyu na tarukan tuntuba a matakin gundumomi domin tattara ra’ayoyin jama’a don shirya kasafin kuɗin Jihar Katsina na shekarar 2027.
A cewarsa, ana gudanar da tarukan ne a lokaci guda a gundumomi 361 da ke cikin ƙananan hukumomi 34 na jihar, domin ƙarfafa shugabanci na bai ɗaya, gaskiya, riƙon amana da kuma bai wa jama’a damar ba da gudunmawa.
Radda ya ce shawarwarin da aka tattara a irin wannan taro da aka gudanar a shekarar 2025 sun taimaka wajen tsara kasafin kuɗin 2026, inda aka fara aiwatar da ayyuka a fannoni kamar gine-ginen more rayuwa, lafiya, noma, ilimi, samar da ruwa, tsaro, bunƙasa matasa da ci gaban al’umma.
Ya amince cewa ba za a iya aiwatar da dukkan buƙatun jama’a a lokaci guda ba saboda ƙarancin kuɗi, amma ya tabbatar da cewa ba za a yi watsi da wata buƙata ta al’umma ba.
Gwamnan ya kuma yi kira ga mata, matasa, masu buƙata ta musamman, manoma, ‘yan kasuwa, masu sana’o’i da ƙungiyoyin al’umma da su shiga cikin shawarwarin domin taimakawa wajen tsara makomar jihar.
A nasa jawabin, Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Alhaji Anas Malik, ya ce dukkan shawarwarin da za a tattara daga gundumomi 361 za a nazarce su tare da duba yiwuwar saka su cikin kasafin kuɗin shekarar 2027 bisa ga albarkatun da gwamnati ke da su da kuma abubuwan da ta bai wa fifiko.