Gwamnatin Jihar Legas ta ba wani jami’in Hukumar Kula da Tsaftar Muhalli ta Jihar (LAGESC) takardar neman bayani bayan wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna ana zargin ya karbi cin hancin naira 20,000 daga wani da ake zargin ya karya dokokin muhalli.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na jihar, Tokunbo Wahab, ya bayyana cewa halayen da ake zargin jami’in ya aikata sun saba da dokoki da ka’idojin aikin gwamnati.
Ya ce an ba jami’in takardar neman bayani, sannan za a kafa Kwamitin Gudanar da Ma’aikata domin gudanar da cikakken bincike bisa tanadin dokokin aikin gwamnati na Jihar Legas.
Wahab ya jaddada cewa gwamnatin jihar ba ta amince da cin hanci ko duk wani nau’in rashin da’a a cikin aikin gwamnati, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
Ya kuma gargadi al’umma da su guji bai wa jami’an gwamnati cin hanci, yana mai cewa bayar da cin hanci da karbarsa duk laifuka ne a gaban doka.
A cikin takardar neman bayanin, an umurci jami’in da ya gabatar da rubutacciyar amsa cikin sa’o’i 48, yana bayyana dalilin da ya sa ba za a dauki matakin ladabtarwa a kansa ba idan har ya kasa kare kansa daga zargin da ake yi masa.
