Majalisar Jarrabawar Yammacin Afirka, WAEC, ta tabbatar da naɗin Suleiman Kum, mai shekaru 56, a matsayin sabon Shugaban Ofishin WAEC na Najeriya (HNO).
Kafin wannan naɗi, Kum ya kasance Mataimakin Magatakarda (Deputy Registrar) a ofishin HNO, sannan ya riƙe matsayin Senior Deputy Registrar mai kula da harkokin gudanar da jarrabawa, har zuwa ƙarshen watan Agustan 2026.
Kum ya maye gurbin Dr Amos Dangut, wanda wa’adinsa na shekaru uku a matsayin shugaban ofishin WAEC na Najeriya ya ƙare a ranar 1 ga Oktoba, 2026. Bayan kammala wa’adinsa, Dangut ya koma matsayin Magatakarda kuma Babban Daraktan WAEC (Registrar/Chief Executive Officer).
Kwarewar Suleiman Kum A WAEC
A cikin wata sanarwa da Shugabar Hulɗa da Jama’a ta WAEC Nigeria, Moyosola Adesina, ta fitar ranar Lahadi, ta bayyana Kum a matsayin ƙwararren masani kan ƙirƙira da gudanar da jarrabawa da kuma shugabanci.
Sanarwar ta ce Kum ya shiga WAEC ne a ranar 17 ga Yuli, 1998, a matsayin Assistant Registrar II, kafin daga bisani ya riƙe manyan mukamai daban-daban a cikin hukumar.
Daga cikin abubuwan da aka yaba masa a kansu akwai jagorantar kirkire-kirkire a fannin fasahar gudanar da jarrabawa da kuma tsaron takardun jarrabawa.
An ce Kum ya taka rawa wajen ƙaddamar da tsarin Variable Data Printing da inganta hanyoyin tsaron lambobi a harkar buga takardu masu muhimmanci.
Haka kuma, ya jagoranci sauya tsarin rajistar halartar ma’aikata a faɗin hukumar zuwa amfani da na’urorin tantance fuska ta hanyar biometric, tare da jagorantar gudanar da wasu jarrabawar Achievement Tests cikin nasara ta hanyar amfani da tsarin Computer-Based Examination.
Mukaman Da Ya Riƙe
Sanarwar WAEC ta ce Kum yana da cikakken ƙwarewa a fannonin ƙirƙira da haɓaka jarrabawa, gudanar da jarrabawa, tsaron jarrabawa, da kuma kula da ofisoshin hukumar na shiyya da yankuna.
A tsawon aikinsa, ya riƙe mukamai da dama, ciki har da:
Assistant Registrar II/Head, Exams Security, Awka;
Assistant Registrar I/Head, Exams Security, Yola;
Assistant Registrar I/Head, Exams Security, Makurdi;
Senior Assistant Registrar I/Branch Controller, Gusau;
Principal Assistant Registrar/Branch Controller, Kano;
Deputy Registrar/Head, Security Printing Department;
Deputy Registrar/Zonal Coordinator, Port Harcourt;
Deputy Registrar/Zonal Coordinator, Ikeja;
Director of Administration;
Senior Deputy Registrar/Test Administration.
WAEC ta kuma bayyana cewa a lokacin aikinsa, Kum ya jagoranci wasu sauye-sauyen gudanarwa da fasaha, ciki har da kafa ofishin Gusau a matsayin Custodial Centre, wato cibiyar kula da muhimman kayayyaki da takardun jarrabawa.
Karatunsa Da Asalinsa
Suleiman Kum ɗan asalin Jihar Plateau ne.
Yana da Postgraduate Diploma in Education daga National Open University of Nigeria (NOUN), kuma a halin yanzu yana karatun Master of Education a fannin Educational Administration and Planning a jami’ar.
WAEC ta ce a tsawon shekarun da ya yi yana aiki a hukumar, Kum ya nuna ƙwazo, gaskiya, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma jajircewa wajen gudanar da ayyukansa.
Hukumar ta ƙara da cewa shugabancinsa a fannoni daban-daban ya sa ya samu yabo, karramawa da lambobin yabo da dama daga cikin hukumar da kuma wajen ta.
Naɗin Kum ya zo ne a lokacin da WAEC ke ci gaba da amfani da sabbin fasahohi wajen inganta tsaron jarrabawa, gudanar da jarabawa da kuma rage matsalolin da ke tattare da harkokin jarrabawa a Najeriya.
