Mutane biyu sun mutu, yayin da ake ci gaba da neman wani mutum da ya bace, bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa mummunar ambaliyar ruwa a yankin Catalonia da ke arewa maso gabashin Spain.
Ambaliyar ta fara tsananta ne tun ranar Asabar, 3 ga Oktoba, inda hukumomi suka bayar da gargadin yanayi mai tsanani tare da umartar mazauna yankunan da abin ya shafa da su zauna a gidajensu tare da gujewa tafiye-tafiye.
Shugaban yankin Catalonia, Salvador Illa, ya tabbatar da mutuwar wani mutum a garin Tordera, da ke arewacin Barcelona, bayan wani bango ya rufta ya fada kansa. Haka kuma, jami’an kashe gobara sun tabbatar da mutuwar wani mutum a Montornès del Vallès.
A garin Pineda de Mar kuwa, ana ci gaba da neman wani mutum da ake zargin ambaliyar ruwa ce ta kwashe shi bayan ya fada cikin wata rafin ruwa.
Ruwan saman ya janyo ambaliyar gidaje, ya mamaye motoci, tare da katse wasu hanyoyin mota da zirga-zirgar jiragen kasa a yankunan da dama da ke kusa da Barcelona.
Hukumomin Catalonia sun ce jami’an kashe gobara sun gudanar da ayyuka har sau 2,440, ciki har da ayyukan ceto guda 226, yayin da lambar gaggawa ta yankin ta karɓi kira 8,151, mafi yawansu na da alaka da ambaliyar ruwa, barazanar rugujewar gine-gine, ayyukan ceto da matsalolin zirga-zirga.
Ambaliyar ta kuma haifar da tsaiko a filin jirgin saman Barcelona, inda aka soke wasu jirage ko aka jinkirta su. Haka kuma, an dakatar da wasu ayyukan jiragen kasa, wasu shaguna suka rufe da wuri, yayin da aka dage wasu wasannin kwallon kafa.
A bangaren nishaɗi kuwa, an soke wani wasan kwaikwayo na opera mai suna Aida a gidan wasan kwaikwayo na Liceu da ke Barcelona saboda tsananin yanayin.
A ranar Litinin, 5 ga Oktoba, jami’an ceto sun sake ci gaba da neman mutumin da ya bace, yayin da hukumomi ke aikin tantance barnar da ambaliyar ta haddasa.
Hukumomin Catalonia sun kuma gargadi jama’a da su ci gaba da taka-tsantsan, saboda ana sa ran sake samun ruwan sama mai ƙarfi a wasu sassan yankin.
A wani lamari dabam da ya faru a tsakiyar Spain, wata mata mai shekaru 102 ta mutu a ranar Asabar bayan ruwan sama mai ƙarfi ya addabi yankin Castilla-La Mancha.
Hukumomi na ci gaba da duba irin barnar da ambaliyar ta yi wa gidaje, hanyoyi da sauran muhimman ababen more rayuwa, yayin da jami’an agaji ke ci gaba da aikin ceto da taimaka wa wadanda abin ya shafa.
