Fitacciyar mawaƙiyar Najeriya, Sarah Aderibigbe, wadda aka fi sani da Ayra Starr, ta samu wani sabon gagarumin matsayi a duniya bayan sabon albam ɗinta, Starrgirl, ya fara shiga Billboard World Albums Chart a matsayi na huɗu.
Wannan nasara ta zo ne kasa da makonni biyu bayan fitar da albam ɗin, wanda aka saki a ranar 14 ga Agusta, 2026, ƙarƙashin Mavin Records da Republic Records.
Rahoton PUNCH Online ya tabbatar da cewa Starrgirl ta kasance ta huɗu a jadawalin Billboard World Albums na makon da ya ƙare a ranar 29 ga Agusta, 2026.
Ayra Starr ta shiga jadawalin ne a bayan ƙungiyoyin K-pop guda uku. Stray Kids da albam ɗinsu This & That sun riƙe matsayi na farko, yayin da GREEN GREEN na CORTIS da Golden Hour: Part.5 na ATEEZ suka kasance na biyu da na uku.
Mawaƙiyar Afirka ta Kudu, Tyla, ita ce ta biyar da albam ɗinta APOP*.
Starrgirl shi ne albam na uku na Ayra Starr, bayan 19 & Dangerous da ta fitar a shekarar 2021, da kuma The Year I Turned 21 wanda ta fitar a 2024.
Albam ɗin mai ɗauke da waƙoƙi 16 ya ƙunshi manyan mawakan Najeriya da na ƙasashen waje, ciki har da Wizkid, Rema, Zayn, Leon Thomas, kwn, Danny Ocean da Theodora.
Baya ga Billboard, albam ɗin ya kuma samu nasarori a wasu jadawalin kiɗa. Ya kai matsayi na 8 a UK R&B Albums Chart, yayin da ya kasance na 27 a UK Album Downloads Chart da kuma na 100 a France SNEP Albums Chart.
A Najeriya kuma, Starrgirl ta hau saman jadawalin albam na Spotify, sannan ta samu matsayi na ɗaya a Apple Music a wasu ƙasashe.
Wannan sabon ci gaba na ƙara nuna yadda Ayra Starr ke ci gaba da kafa kanta a matsayin ɗaya daga cikin fitattun mawakan Najeriya da ke samun karɓuwa a fagen kiɗan duniya.
Ku ci gaba da kasancewa tare da ASRAH 24 TV domin samun ƙarin labaran nishaɗi da na mawakan Najeriya.
