Gwamnan Jihar Cross River, Bassey Otu, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ƙara ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya, duk da bambance-bambancen ƙabilanci, addini, harshe da al’adu da ke tsakanin al’ummar ƙasar.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a yayin wani taron addu’a da godiya na addinai daban-daban da aka gudanar a ranar Lahadi a Christian Central Chapel International (CCCI), wanda aka fi sani da Faith Mansion, da ke Ikot Enebong, 8 Miles, Calabar.
An gudanar da taron ne domin bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kan Najeriya, inda manyan jami’an gwamnati, shugabannin addinai da dubban masu ibada suka halarta.
Gwamna Otu, wanda Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Cross River, Elvert Ayambem, ya wakilta, ya ce ya kamata ƴan Najeriya su ɗauki bambance-bambancen da ke tsakaninsu a matsayin wata dama da za ta ƙara ƙarfafa ƙasar, ba wani abu da zai raba su ba.
Ya ce:
“Bambance-bambancenmu bai kamata ya raba mu ba. Najeriya tamu ce gaba ɗaya, kuma ƙarfinmu yana cikin ikonmu na karɓar bambance-bambancen da ke tsakaninmu yayin da muke aiki domin cimma manufofin da suka shafe mu baki ɗaya.”
Gwamnan ya bayyana cewa shekaru 66 bayan samun ‘yancin kai, Najeriya ta fuskanci lokutan da ke cike da fata, wasu lokutan ƙalubale da kuma sauye-sauye masu yawa, amma juriyar al’ummar ƙasar ta taimaka wajen ci gaba da riƙe ƙasar a matsayin ƙasa ɗaya.
Ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa wajen ci gaba da aiwatar da People First Agenda, wadda ya ce ta mayar da hankali ne kan inganta rayuwar jama’a, samar da damarmaki ga matasa, ƙarfafa harkar ilimi da kiwon lafiya, da kuma inganta ababen more rayuwa.
Otu ya buƙaci al’ummar Cross River da sauran ƴan Najeriya su ci gaba da kasancewa masu fata, tare da ƙin tashin hankali da rarrabuwar kawuna.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su taka rawar gani wajen gina ƙasa, tare da yin addu’ar Allah Ya ba shugabannin ƙasar hikima, Ya kawo zaman lafiya a cikin al’ummomi, sannan Ya ba iyalan da ke fuskantar matsaloli ƙarfin zuciya da sauƙi.
Archbishop Isong Ya Yi Gargadi Kan Kalaman Da Za Su Tayar Da Hankula
Shi ma limamin da ya jagoranci taron, kuma Mataimakin Shugaban Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) na shiyyar Kudu maso Kudu, Archbishop Emma Isong (JP), ya yi kira ga ƴan Najeriya da su guji sukar shugabannin ƙasar ba tare da wani dalili mai ma’ana ba.
Isong ya kuma yi gargadi ga shugabannin siyasa da sauran masu riƙe da mukaman gwamnati da su guji furta kalaman da ka iya ƙara tayar da hankali ko haifar da rarrabuwar kai a tsakanin al’umma.
Ya ce:
“Dole ne shugabanni su kula da abin da suke faɗa, domin mukamai suna da wa’adi.”
Ya bayyana cewa a tsarin dimokuraɗiyya, ƴan ƙasa suna da damar yin suka ga gwamnati, amma bai kamata a mayar da shugabanni tamkar masu aikata laifi ba.
Ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su guji riƙe ƙiyayya da rashin yafiya, tare da ƙarfafa yin sulhu da sasanta bambance-bambance.
Archbishop Isong ya kuma gargadi jama’a da su daina murna idan wani ya fuskanci gazawa ko matsala, yana mai cewa:
“Ba za ka yi wa maƙwabcinka addu’ar faɗuwa ba, sannan ka durƙusa kana roƙon Allah Ya ɗaukaka ka.”
Ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ƙara nuna wa juna tausayi, haɗin kai da fahimtar juna domin samun zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
