Kungiyar Afenifere ta yi gargadin cewa yawaitar sace manoma da kai musu hare-hare a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya na barazana ga noma da samar da abinci.
Kungiyar ta ce wasu manoma sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron a sace su, karancin farashin amfanin gona da kuma kutsen makiyaya cikin gonaki.
Afenifere ta bayyana cewa hare-haren na kuma hana masu zuba jari shiga harkar noma, tare da rage yawan amfanin gona da jefa dubban iyalan manoma cikin matsala.
Saboda haka, kungiyar ta bukaci gwamnoni shida na Kudu maso Yamma da su kara karfafa Amotekun, samar masa da motocin aiki, kayan sadarwa da jiragen leken asiri, tare da kafa rundunonin musamman domin sintiri a dazuzzukan da masu aikata laifuka ke fakewa.
Ta kuma bukaci a kara tsaurara tsaron iyakokin jihohi, hada kan jami’an tsaro da mafarauta da kungiyoyin sa-kai wajen tattara bayanan sirri, tare da tabbatar da dokokin hana kiwo a fili.
Afenifere ta yi gargadin cewa idan ba a dauki matakin gaggawa kan matsalar tsaro ba, Najeriya na iya fuskantar karancin abinci da kara tabarbarewar tattalin arzikin manoma.
