Kwamitin musamman da ke binciken Museum of West African Art (MOWAA) a Jihar Edo, karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole, ya ba da shawarar cewa a mayar da kula da gidan tarihin hannun Oba na Benin.
Oshiomhole ya ce binciken kwamitin ya nuna cewa gwamnatin tsohon gwamna Godwin Obaseki ta kashe kusan Naira biliyan 3.8 na kudaden jama’a wajen aikin gidan tarihin.
Ya kuma ce asalin shirin shi ne gina Benin Royal Museum, domin adana kayayyakin tarihi na Benin da ake kokarin dawo da su daga kasashen waje.
Sai dai a cewar kwamitin, daga baya aka sauya sunan da manufar aikin zuwa Edo Museum of West African Art, sannan daga bisani aka mayar da shi Museum of West African Art – MOWAA.
Kwamitin ya ba da shawarar a mayar da sunan gidan tarihin zuwa Benin Royal Museum of African Art, tare da ba Oba na Benin damar kula da shi.
Oshiomhole ya ce hakan zai fi dacewa domin gwamnati tana sauyawa, amma masarautar Benin tana nan, kuma za a iya kare kayayyakin tarihin yadda ya kamata a karkashin cibiyar da ta mallake su.
Gwamna Monday Okpebholo ya yabawa kwamitin kan rahoton da ya gabatar, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta kafa wani kwamiti tare da Ma’aikatar Shari’a domin shirya White Paper kan shawarwarin kwamitin.
