Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi hasashen cewa za a samu babbar kawancen siyasa daga ‘yan siyasa daban-daban domin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaben shugaban kasa na 2027.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin da yake duba ayyukan raya birnin.
Ya danganta ziyarar da Gwamnan Osun mai jiran gado, Ademola Adeleke, ya kai wa Tinubu da wani sabon sauyi a siyasar Najeriya.
A cewar Wike, wannan sabon hadin kai zai samar da abin da ya kira “babbar Rainbow Coalition”, wadda za ta kunshi ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban da ke goyon bayan Tinubu.
Wike ya ce nan da makonni masu zuwa, “za a ga wata babbar Rainbow Coalition a Najeriya tana goyon bayan Shugaba Tinubu.”
Ministan ya kuma yi watsi da ikirarin wasu ‘yan jam’iyyar ADC cewa sun taimaka wajen nasarar Adeleke, yana mai cewa suna kokarin cin moriyar nasarar da ba su shuka ba.
Wike ya kuma ce babu wata jam’iyyar adawa da za a iya cewa ita ce babbar adawa a Najeriya a halin yanzu, yana mai cewa rikicin cikin gida ya raunana PDP.
Ya kara da cewa manufarsa ita ce ganin bangarensa ya yi nasara a siyasa, domin a cewarsa, siyasa ba wasa ba ce da ake yi domin faranta ran abokan hamayya.
