Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya mayar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu martani kan kalaman da ya yi game da shirin Atiku na kawo sabon tsari a ɓangaren man fetur.
Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da jefa ƴan Najeriya cikin ƙarin tsadar rayuwa tun bayan cire tallafin man fetur, inda ya ce farashin mai, sufuri da kayan abinci sun yi tashin gwauron zabi.
Ya bayyana cewa shirin da yake gabatarwa ba wai dawo da tsohon tsarin tallafin man fetur ba ne, sai dai wani tallafi na wucin gadi da aka tsara domin ƙara samar da man fetur a cikin gida tare da rage wa ƴan Najeriya radadin tsadar mai.
Atiku ya kuma tambayi gwamnati cewa idan an kawo ƙarshen tallafin mai, “me ya sa har yanzu ake samun wasu kudade na under-recovery a bangaren man fetur?”
Ya ce bai kamata a dauki karin kudaden da gwamnati ke samu a matsayin nasarar tattalin arziki ba, idan a lokaci guda talakawan Najeriya na ci gaba da rasa karfin sayayya.
Atiku ya kuma nemi gwamnati ta yi karin bayani kan kudaden da ya ce sun kai kusan Naira tiriliyan 30 na kudaden Federation Account, tare da tambayar yadda aka sarrafa wasu manyan kudaden da ke cikin kasafin kudin 2026.
A karshe, Atiku ya ce nasarar gyaran tattalin arziki bai kamata a auna ta da yawan kudin da gwamnati ke tarawa ba, sai da irin saukin da talakawa ke samu a rayuwarsu.
