Hukumar FBI ta Amurka ta nemi izinin wata kotu da ke Washington, D.C., domin gabatar da bayanan sirri da ke bayyana dalilin da ya sa take ƙin sakin wasu bayanai da suka shafi binciken da aka yi kan zargin da ya danganta Shugaba Bola Ahmed Tinubu da wani binciken safarar miyagun ƙwayoyi.
FBI ta ce sakin wasu daga cikin bayanan na iya tona dabarun binciken jami’an tsaro ko kuma jefa rayuwar wasu mutane cikin haɗari.
Hukumar ta kuma nemi ta gabatar da bayanan cikin sirri ga alkalin kotun, ba tare da sanya su a cikin bayanan jama’a ba.
Batun ya samo asali ne daga buƙatar wani Ba’amurke mai suna Aaron Greenspan, wanda ya nemi bayanan FBI da suka shafi Tinubu da kuma wasu fayilolin bincike na shekarun 1992 zuwa 1993.
Lamarin ya sake ɗaukar hankali ne yayin da ake ci gaba da shari’ar da Greenspan ya shigar yana ƙalubalantar matakin hukumomin Amurka na ɓoye ko tabbatar da kasancewar wasu bayanai.
A shekarar 2025, Alƙali Beryl Howell ta ce FBI da DEA ba su bayar da isasshen hujjar ci gaba da amfani da matakin da zai hana bayyana ko akwai irin waɗannan bayanan.
Sai dai a sabon matakin, FBI na neman kotun ta amince mata da gabatar da ƙarin bayanan sirri domin kare wasu bayanan da ta ce ba za ta iya bayyana dalilinsu a bainar jama’a ba.
