An binne gawar fitaccen jarumin Nollywood, Taiwo Hassan, wanda aka fi sani da Ogogo, a garinsu na Ilaro, Jihar Ogun.
An yi jana’izar ne ranar Litinin, cikin alhini da kuka, yayin da ’yan uwa, abokan aiki, abokai da mazauna garin suka taru domin yin bankwana da fitaccen jarumin.
Daga cikin fitattun jaruman da suka halarci jana’izar akwai Yinka Quadri, Jide Kosoko, Fausat Balogun, Toyosi Adesanya da Femi Adebayo, wadanda suka zo domin karrama abokin aikinsu da suka dade tare.
Rahotanni sun ce Taiwo Hassan ya rasu ne ranar Lahadi, 23 ga Agusta, 2026, yana da shekaru 66, bayan fama da cutar kansa mai matakin ƙarshe.
Rasuwarsa ta jawo jimami a masana’antar Nollywood, musamman tsakanin jaruman da suka yi shekaru suna aiki tare da shi.
