Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan wasu dokoki guda hudu da suka kafa sabbin hukumomi da aka tsara domin karfafa tsarin hukumomi da kuma kara kaimi wajen samar da ci gaba mai dorewa a fadin jihar.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Alhamis.
SolaceBase ta ruwaito cewa sabbin dokokin da aka sanya wa hannu sun tanadi kafa hukumomin kamar haka: Hukumar sanya idanu kan hukumomin gwamnati a ihar Kano (KASPA), hukumar kula da Tallace-tallace ta Jihar Kano (KASIAA), hukumar bunkasa harkokin yada labarai da fasahar sadarwa ta jihar Kano (KASITDA) da hukumar bunkasa ƙanana da matsakaitan masana’antu ta jihar Kano (KASMEDA).
A cewar sanarwar, wadannan dokoki wadanda a yanzu suke cikin tsarin dokokin jihar Kano, ana sa ran za su zaburar da ci gabada tallafa wa masu kananan sana’o’i, da daidaita sa hannu a tallace-tallace, da inganta bada kariya da hidima hidima ga jama’a.
“Gwamna Yusuf ya bayyana rattaba hannun a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da manufofin gwamnatinsa na mayar da Kano ta zamani, mai hade da tattalin arziki, in ji sanarwar.
Ya jaddada cewa sabbin hukumomin za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi, jawo masu zuba hannun jari, da aiwatar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.
Ya kuma yi gargadin cewa karya dokokin wadannan hukumomi daidai yake da fuskantar hukunci mai tsauri, yana mai jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da bin doka da oda.
A cewar sanarwar, kafa wadannan hukumomi ya nuna irin kokarin da Gwamna Yusuf ya yi na gyara cibiyoyin gwamnati, da inganta harkokin mulki, da kuma sanya Kano a matsayin babbar cibiyar kirkire-kirkire, kasuwanci, da ci gaba mai dorewa.
