Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja yau zuwa kasashe biyu, wato Japan da Brazil, kamar yadda jaridar Daily Trust ta gano jiya.
Bayo Onanuga, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsara Dabaru, ya ce cikin wata sanarwa cewa a yayin da yake Japan, Shugaba Tinubu zai halarci Taron Hadin Gwiwar Bunkasa Nahiyar Afirka karo na Tara (TICAD9) a Birnin Yokohama daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Agusta.
Daga nan kuma zai wuce Brazil, ƙasa da ya ziyarta sau uku cikin watanni tara da suka gabata.