Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da Shugaban ƙaramar hukumar Rano, Muhammad Nazir Yau tsawon wata uku domin gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da suka haɗa da amfani da ofis ta hanyar da ba ta dace ba da aikata ba daidai ba, da kuma karkatar da kayan mutane.
Kansilolin ƙaramar hukumar ne dai suak shigar da ƙorafinsu gaban majalisar dokokin jihar game da zarge-zargen.
Dakatartwar ta zo ne bayan gabatar da rahoton kwamitin sauraron koke-koken alʼumma ƙarƙashin shugaban masu rinjaye a majalisar, Hon. Lawan Hussaini yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
Wasu daga zarge-zargen da ake yi wa shugaban ƙaramar hukumar ta Rano sun haɗa da ingiza rashin haɗin kai tsakanin shugabannin siyasa da kansilolin ƙaramar hukumar, da kuma rarraba kayan tallafin gwamnati ga abokan siyasarsa kaɗai, da kuma sayar da takin gwamnati kan sama da Naira 20,000 da aka ƙayyade.
Majalisar ta kuma umarci maʼaikatar harkokin ƙananan hukumomi da masarautu ta Kano ta umarci mataimakin ƙaramar hukumar ya shugabance ta zuwa lokacin da za a kammala binciken.
