Gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da wani kwamiti na musamman don yaƙi da matsalar tamowa da rashin abinci mai gina jiki ga ƙananan yara a jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Ibrahim Kaula Muhammad ya fitar, gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne yayin zaman majalisar zartarwar jihar a ranar Laraba.
A farkon makon nan ne ƙungiyar agaji ta likitoci ta Médecins Sans Frontières ta fitar da wani rahoto da a ciki ta ce Katsina ce kan gaba a fama da matsalar tamowa wadda ta kashe ɗaruruwan yara a jihar
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya nemi kwamitin ya yi bincike na tsanaki kan rahoton ƙungiyar agaji ta Médecins Sans Frontières.
Kazalika gwamnan ya nemi kwamitin ya yi nazari na tsanaki kan abubuwan da ke janyo tamowa kamar rashin samar da isashen abinci, da kuma abubuwan da suka shafi zamantakewar aure.
Kwamitin mai mutane 15 na ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar zakka da waƙafi ta jihar, Abdulrahman Abdullahi, tare da sauran jamiʼan gwamnati da kuma wakilan ƙungiyoyin addini, tare da wakilci daga ƙungiyar MSF.