Jakadan ƙasar Belgian a Najeriya, Pieter Leenknegt, ya ce matatar man Dangote za ta shafi harkar shigo da tataccen mai Najeriya daga ƙasarsa da ma tsarin kasuwanci a tsakanin ƙasashen na wani lokaci.
Kafin fara aikin matatar man Ɗangote, Najeriya na kan gaba wajen shigo da man fetur daga kasar Belgium.
Sai dai matatar man Ɗangote wacce ta fara aiki a shekarar bara, ta yi iƙirarin cewa za ta iya samar da man da ake buƙata a Najeriya.
A cikin wata tattaunawa ta musamman da PREMIUM TIMES ta yi da mista Leenknegt, ya ce, ana ganin fara tace mai da Najariya ta yi zan rage yawan man da take shigo da shi daga Belgium sosai.
Ya bayyana hakan da “tasirin da kamfanin Ɗangote ke da shi” yana mai nuna babban giɓin da ƙasarsa za ta samu tsakaninta da Najeriya duk da kasancewarta ƙasa da ke sahun masu samar wa da ƙasar nan man fetur.
Ya ce, ana tunanin za a fara ganin wannan tasiri a kasuwancin kasashen biyu ne daga karshen shekarar 2025.
“A fili yake cewa (ayyukan matatar Ɗangote), na wani lokaci zai shafi kasuwancin da ke tsakanin ƙasashen nan biyu,” ya faɗa.
Duk da a shekarar 2024 an samu raguwar man da Najeriya ke saye daga kasar Belgium, jakadan ya alaƙanta hakan da rage amfani da makamashi da aka yi a ƙasar nan a maimakon cewa tasirin matatar Dangote ce.
“An samu raguwar fitar da kaya daga Belgium zuwa Najeriya, haka ma daga Najeriya zuwa Belgium,” ya bayyana.
“Amma ba tasiri matatar man Dangote ba ce. Batu ne na yanayin sayen makamashi a Najeriya wanda ya sa ‘yan ƙasar ba su da wadataccen Dala ko Yuro a hannunsu da za su bi sayi kaya daga waje.”
A yayin da yake nuna amincewarsa da rawar ƙasarsa na mamaye harkar shigo da mai Najeriya, jakadan ya ce, “mu ne kasar nahiyar Turai mafi shigo da kaya Najeriya, kuma mafi yawa danyen man fetur ne.”
Kusan kaso 40% na abin da Najeriya take saye daga waje yana wucewa ne ta Belgium, kuma yawanci tataccen man fetur ne.
Kuma Belgium babbar mai samar wa da Najeriya sinadarai ce da kayan kiwon lafiya da kayan amfani a masana’antu.
Game da matatar man Dangote:
Matatar man Dangote ita ce mafi girma a duniya wajen tace mai, kuma ta fara ne da ta ce man dizal da man jirgin sama a watan Janairun 2024 amma sai a Satumbar 2024 ta fara tace man fetur.
Fara aikin matatar ya jawo raguwa yawan man da ake shigo da shi Najeriya. Kuma ya jawo an rage kashe kuɗin waje.
A cewar hukumar kididdiga ta ƙasa (NBS), rahotanni sun nuna cewa Najeriya ta kashe Dala biliyan 1.2 wajen shigo da mai a rubu’in farko na shekarar 2025 ƙasa da Dala biliyan 2.6 da ta kashe a bara.
A watan Yuni, matatar ta sanar da fara sayar da man fetur da dizal ga ‘yan kasuwa da kamfanoni da kamfanonin sadarwa .da sauran masu sayen mai da yawan gaske.
A cikin watanni uku, matatar Dangote ta rage yawan farashin manta har sau biyu domin yin daidai da farashin mai a duniya. Da farko, a watan Yuni, daga N880 zuwa N840 na kowanne lita. Sai kuma a watan Yuli zuwa N8320 kowanne lita.
Kafin samar da kamfanin matatar Dangote, Najeriya ta dogara ne da shigo da mai daga kasar waje duk da ita ce kan gaba wajen samar da ɗanyen mai a Afirka.
Mista Leenknegt ya bayyana yawan dogaro da shigo da tataccen mai Najeriya da rashin kan gado.
“Ba lissafi a tafi da mai Turai daga Najeriya sannan a sake dakonsa daga Turai zuwa Najeriya. Ba lissafi sosai.”
“Daga lokacin da Najeriya ta iya samar da ingantaccen tataccen man fetur, wacce kuma kasar Belgium da za ta ƙalubalance ta?” Ya tambaya.
“Amma abin da za mu mai da hankali a kai shi ne kasuwancinmu da Najeriya zai karkata ne kan wasu abubuwa a nan gaba.”
Misata Leenknegt, ya ce Belgium tana tunanin karkata harkar shigo da kayan zuwa Najeriya daga harkar man fetur zuwa ga harkar noma.
Ya ce wannan sauyi wata hanya ce ta sauya kalar kasuwanci da Belgium ke shirin yi tsakaninta da Najeriya.
“Mun daɗe muna tunanin sake fasalin kasuwancinmu tun da daɗewa daga man fetur zuwa wani abu daban saboda bai kamata ƙasa ta ta’allaka tattalin arziƙinta da dogaro da mai ba,” ya faɗa.
A cikin wannan hira, jakadan ya tattauna wasu abubuwa da suka shafi samar da magunguna da noma da sauran harkokin kasuwanci.