Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kori wasu hadimansa biyi masu taimaka masa na musamman biyo bayan sakamakon kwamitin bincike da aka kafa domin bincikar kowannensu.
Wanann na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Kano, Umar Farouk Ibrahim, ya fitar a ranar Asabar.
Sakamakon wancan bincike, gwamnan ya amince da sallamar Abubakar Umar Sharada, babban mai taimaka masa kan harkokin siyasa bayan kwamitin bincike ya same shi da hannu wajen belin babban dilan ƙwaya Sulaiman Aminu Danwawu.
Kwamitin ya bankaɗo yadda Sharada ya bayar da shaida ta ƙashin kansa kan wannan gagarun dilan kwayan.
A cewar wasiƙar da sakataren gwamnatin Kano (SSG), ya fitar a ranar Juma’a, 8 ga Agustan 2025, an buƙaci Sharada ya miƙa dukkan kayan gwamnati da ke hannunsa ga sakataren dindin na ofishin mai bincike da tantancewa da harkokin siyasa (REPA) da ke ƙarƙashin ofishin sakataren gwamnatin, a ranar ko kafin Litinin, 11 ga watan Agustan 2025.
Sannan ana gargaɗinsa da kiran kansa da jami’an wannan gwamnati a ko’inna.
Haka kuma, gwamnan Kano ya sauke Tasiu Adamu Al’amin Roba, babban mai taimaka masa kan tafiyar da al’amuran gwamnat (Cabinet Office) bayan samunsa da laifin sauya buhunhunan hatsi na tallafi da ke ajiye a ɗakin ajiya a Sharaɗa tun a shekarar 2024.
Tun wannan lokaci ne Roba ke fuskantar shari’a a kotu bisa zargin laifin sata da haɗa kai wajen aikata babban laifi na karkatar da kayan gwamnati.
Shi ma Roba, an buƙaci ya miƙa duk wani abin amfani na gwamnati da ke hannunsa haɗi da shaidar fayyace kai (ID card) , a ranar ko kafin Litinin 11 ga watan Agustan 2025. Sannan ana gargaɗinsa da kauce wa kiran kansa da jami’in gwamnatin jihar Kano.
A wani makamancin al’amari, gwamnatin Kano ta wanke Hon. Musa Ado Tsamiya, babban mai taimaka wa gwamna kan magudanan ruwa daga zargin da ake yi masa wanda kwamitin binciken ya tabbatar cewa bai aikata kowanne irin laifi.
Gwamna Abba ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta tabbatar da ɗa’a da gaskiya da cewa ba za ta lamunci kowanne irin nau’i na cin hanci da rashawa ba.
Ya kuma gargaɗi dukkan masu riƙe da muƙamai da yi riƙo da gaskiya a dukkan ayyukansu da suka shafi gwamnati da kuma na ƙashin kansu.
“Da wannan sanarwa, ana shawartar al’umma da su guje wa yin kowacce iriyar mu’amala da tsofaffin masu taimaka wa gwamnan da aka kora, musamman abin da ya shafi gwamnati. Kuma duk wanda ya yi hakan, to kar ya zargi kowa, sai kansa.