Ƙaramin Ministan ma’aikatar jin-ƙai da rage talauci, Dr Yusuf Sununu ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma jami’an gwamnati a Abuja.
Sununu ya sanar da cewa za a sake kaddamar da shirin ne domin murnar cikar shugaba Bola Tinubu shekara ta biyu akan karagar mulki.
Ya ce shirin na da nufin magance yunwa da kuma inganta ɓangaren ilimi a faɗin ƙasa baki ɗaya.
A cewar sa, sake ƙaddamar da shirin na zuwa ne a daidai lokacin da ake hasashen cewa sama da ƴan Najeriya miliyan 30 na iya fuskantar matsananciyar yunwa, wanda hakan ke nuni da muhimmancin ɓullo da shirye-shirye makamantan wannan cikin gaggawa.
