Masana harkokin fasahar zamani sun gargadi bankuna a Najeriya da sauran kasashen Afirka cewa zuba jari a fannin basirar na’ura (Artificial Intelligence – AI) ba zai samar da sakamakon da ake bukata ba idan ba a gina shi kan ingantattun bayanai da tsarin adana su yadda ya kamata ba.
Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da bankuna ke kara amfani da fasahar AI wajen gano damfara, tantance masu neman rance, inganta hulda da kwastomomi da kuma kara ingancin gudanar da ayyuka.
A cewar wani rahoto da kamfanin samar da fasahar banki na Oradian ya wallafa mai taken “The Digital-First Bank’s Guide to AI in 2026,” nasarar duk wani shirin AI tana dogara ne sosai kan inganci da saukin samun bayanan da tsarin ke amfani da su.
Rahoton ya nuna cewa kusan kashi 95 cikin 100 na ayyukan AI da bankuna ke aiwatarwa suna fuskantar gazawa saboda rashin mayar da hankali kan muhimmancin ingantaccen tsarin bayanai.
Masana sun bayyana cewa duk da biliyoyin dalolin da cibiyoyin hada-hadar kudi ke kashewa wajen bunkasa AI, da dama daga cikinsu na fama da matsalolin rarrabuwar bayanai a wurare daban-daban, rashin kyakkyawan tsarin kula da bayanai da kuma tsofaffin tsarin gudanar da ayyukan banki.
A cewar rahoton, wadannan matsaloli ne ke hana fasahar AI yin aiki yadda ya kamata tare da rage amfanin da ake sa ran samu daga gare ta.
Masana sun kuma bayyana cewa AI na da damar sauya tsarin banki ta hanyar saurin yanke hukunci, kyautata hulda da kwastomomi, sarrafa ayyuka ta atomatik da kuma inganta kula da hadurra. Sai dai suna jaddada cewa hakan ba zai yiwu ba sai idan an samar da ingantaccen tsarin dijital da zai iya daukar nauyin manyan bayanai da tsarin koyon na’ura.
Rahoton ya yi hasashen cewa cibiyoyin banki a duniya za su kashe kusan dala biliyan 97 wajen gina tsarin AI nan da shekarar 2027 domin bunkasa kirkire-kirkire da kara gasa a kasuwa.
Sai dai masana sun yi gargadin cewa kashe makudan kudade a AI ba tare da saka jari a ingancin bayanai, hade bayanai da tsarin tafiyar da su ba na iya zama asarar kudi mai yawa.
Rahoton ya bayyana cewa, “Duk wani tsarin AI yana dogara ne da bayanai. Inganci da saukin samun bayanai ne ke iya tabbatar da nasara ko gazawar kowanne aikin AI.”
Masu nazari sun kara da cewa babban kalubalen da ke gaban bankuna ba rashin sha’awar amfani da AI ba ne, illa raunin tsarin aiwatarwa da kuma rashin kyakkyawan tushe na fasaha.
Sun bayyana cewa bankunan da suka samu nasarar amfani da AI su ne wadanda suka fara sabunta tsarin bankinsu, suka kafa ingantaccen tsarin kula da bayanai tare da tabbatar da samun sahihan bayanan kwastomomi da ayyukansu cikin sauki.
A Najeriya, wannan gargadi na zuwa ne yayin da bankuna ke kara rungumar tsarin dijital domin ci gaba da kasancewa cikin gasa a duniyar hada-hadar kudi mai saurin sauyawa.
Masana sun yi imanin cewa bankunan da za su mayar da hankali wajen inganta tsarin bayanansu tare da zuba jari a AI za su fi samun damar cin gajiyar sabbin fasahohi tare da kara ribar kasuwanci na dogon lokaci.
