Gwamnatin tarayya ta ce faduwar dalibai da aka samu a jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandare ta kasa JAMB a bana na nuni da yadda gwamnati ke daukar matakan magance magudin jarrabawa musamman ta JAMB a kasar.
Ministan Ilimi Dakta Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a wata hira da akayi da shi a gidan Talabijin na Channels.
Ya kuma ce kaso 78 na daliban da suka zauna jarrabawar ba zasu iya cin maki sama da dari biyu ba, wanda hakan ke nuni karara da yadda kokarin dalibi zai iya sawa ya tsallake jarrabawar.
Kazalika ya ce za su kara fito da hanyoyi masu kyau a jarrabawar NECO da WAEC da dalibai ke zaunawa a kasar nan dan ganin an tantance masu hazaka a cikin su.
