Gwamnatin tarayya ta sakarwa malamai da ma’aikatan jami’oin kasar nan kudaden alawus alawus din da suke binta na naira biliyan 50.
Hakan na zuwa ne a wani bangare na alkawarin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi musu na biyan su hakokin nasu.
Ministan Ilimi Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da Daraktan sashin yada labarai na ma’aikatar Boriowo Folasade ya fitar.
Sanarwar ta kuma ce, hakan na da nasaba da irin kokarin da shugaban kasar yake wajen samar da jin dadi da walwalar malamai da ma’aikatan Jami’oin.
Dakta Alausa, gwamnatin shugaban kasa Tinubu za ta ci gaba da samar da kayan aiki da gine gine a makarantun don inganta Ilimin jami’oin na Najeriya.
