Shirin Hidimar Matasa na Ƙasa (NYSC) ya bayyana cewa zai fara biyan sabon alawus na N77,000 ga ‘yan hidima daga watan Fabrairu na shekarar 2025.
Daraktan Janar na NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin da yake jawabi ga ‘yan Batch ‘C’ Stream II na shekarar 2024 a Katsina.
Ya bayyana cewa wannan ƙaruwa daga N33,000 da ake biya a halin yanzu na cikin kasafin kuɗin gwamnatin tarayya na 2025, kuma za a fara biyan ta da zarar an amince da kasafin.
Ahmed ya tabbatar da cewa gwamnati na da ƙudurin inganta jin daɗin da tsaron ‘yan hidima, yana mai kira da su jajirce wajen yi wa ƙasa hidima. Ya kuma tabbatar musu cewa ba za a tura kowane ɗan hidima zuwa yankunan da ke da matsalar tsaro ba.
source:Dailynews24.ng.com
By: