Dakarun Operation HADIN KAI sun kama wata ‘yar kasar Chadi mai suna Rachael Samuel, mai shekaru 48, bisa zargin safarar kwayoyi da sauran haramtattun kayayyaki zuwa yankunan da ake zargin ‘yan ta’adda ke boye a tsibiran Tafkin Chadi.
A cikin wata sanarwa, jami’in yada labarai na rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce an kama matar ne a ranar Alhamis yayin wani samame da aka gudanar a hanyar Maiduguri zuwa Monguno, tana kan hanyarta zuwa Kwatan Doron Baga da ke karamar hukumar Kukawa a Jihar Borno.
Binciken farko ya nuna cewa ana zargin kayayyakin da aka kama na kan hanyarsu zuwa yankunan Tafkin Chadi, inda ake zargin kungiyoyin ‘yan ta’adda ke gudanar da ayyukansu.
Kayayyakin da aka kwato sun hada da buhuna bakwai na tabar wiwi da nauyinsu ya kai kimanin kilo 30, kwalabe biyu na sinadarin Hydromercuric Chloride (Suck and Die), kwali guda dauke da kwalabe 48 na giya, da kwalabe 61 na wasu abubuwan sha masu dauke da barasa.
Sojojin sun kuma kwato wayar hannu, katunan ATM guda biyu, wasu kayayyaki na sirri da kuma kudi, inda aka ce darajar kayayyakin da aka kama ta kai miliyoyin naira.
Rundunar ta bayyana cewa matar na tsare a hannunta, yayin da za a mika kayayyakin da aka kwato ga hukumomin da abin ya shafa domin ci gaba da bincike da gurfanar da ita a gaban kotu.
Operation HADIN KAI ta ce wannan nasara na daga cikin kokarin da ake yi na katse hanyoyin samar da kayan aiki da tallafi ga kungiyoyin ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabashin Najeriya.
