Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya bukaci a soke sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar Rivers, inda ya bayyana shi a matsayin “abin kunya da cin fuskar tsarin dimokraɗiyya.”
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, Atiku ya caccaki yadda aka gudanar da zaɓen, yana mai cewa:
“Yadda aka gudanar da wannan zaɓe ya nuna cewa jam’iyyar APC tana shirin keta doka don cimma burin siyasa.”
Ya kuma gargadi ‘yan Najeriya da ƙungiyoyin duniya game da “ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na karkatar da Najeriya zuwa turba mai haɗari.”
Atiku ya bukaci jam’iyyun adawa a Rivers su ƙi amincewa da sakamakon, yana mai jaddada cewa “gwamnatin ba ta da hurumin gudanar da zaɓen.”
Sai dai a cewar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Rivers (RSIEC), jam’iyyar APC ta lashe ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23, yayin da PDP ta samu guda uku.