Batun sake nazarin albashin masu riƙe da mukaman siyasa a Najeriya na ci gaba da tayar da ƙura a ƙasar.
Hakan na zuwa ne bayan hukumar raba arzikin ƙasa ta Najeriya (RMAFC) ta sanar da cewa ta fara shirin sake nazarin yadda ake rarraba arzikin ƙasa tsakanin matakan gwamnatin tarayya da jihohi da kuma ƙananana hukumomin ƙasar.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, shugaban hukumar ta RMAFC Mohammmed Shehu ya yi iƙirarin cewa albashin da masu riƙe da mukaman siyasa ke karɓa bai taka kara ya karya ba, yayin da kuma ake fama da matsin tattalin arziki a ƙasar.
Shugaban ya ce a halin da ake ciki yanzu shugaba Bola Tinubu na karɓar naira miliyan 1.5 ne kowanne wata, yayin da abin da ministoci ke karɓa bai kai naira miliyan ɗaya ba.