Shigowar jari zuwa Najeriya ya kai dala biliyan 5.6 a farkon kwata na shekarar 2025, in ji rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS).
Wannan shigowa na nuna babban ci gaba sakamakon gyare-gyaren da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya aiwatar domin sanya ƙasar ta zama wuri mai jan hankalin masu saka hannun jari na cikin gida da na waje.
A cewar masana da dama, shigowar dala biliyan 3.1 zuwa bangaren banki, wanda ya kai kashi 55.44% na dukkan shigowar jarin, na nuna yadda kwanciyar hankalin harkokin kuɗi ke ƙarfafa masu saka hannun jari wajen zuba jari a tattalin arzikin cikin gida.