Hukumar Shirya Fina-Finan Najeriya (NFC) ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Manajan Darakta/Kwamishinan Hukumar, Dakta Ali Nuhu, ya rasu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, 18 ga Agusta, 2025, Hukumar ta bayyana rahotannin — har ma da bidiyoyin da ke yawo da hotunan jarumin
NFC ta tabbatar wa jama’a cewa Dakta Ali Nuhu, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada a ranar 12 ga Fabrairu, 2024, yana cikin koshin lafiya, kuma yana ci gaba da gudanar da aikinsa na hukuma yadda ya kamata.