Mummunan al’amari ya auku a unguwar Hotoron Yan Dodo, ƙaramar hukumar Tarauni, jihar Kano, inda cutar mashaƙo (diphtheria) ta yi sanadiyar mutuwar yara huɗu ‘yan gida ɗaya a cikin makonni biyu kacal.
Mahaifin yaran, Malam Yusuf Maitama, ya bayyana cewa ƙaddarar ta fara ne da ƙaramin ɗansa mai ƙasa da shekaru biyar, wanda ya fara fama da zazzaɓi da ciwon maƙogwaro kafin daga bisani ya rasu. Sai kuma sauran uku daga cikin ‘ya’yansa suka biyo baya da irin waɗannan alamomi, duk da ƙoƙarin ceto su, amma suka rasu. Ita kaɗai babbar ‘yarsa ce ta tsira bayan an kai ta asibiti cikin gaggawa.
Rahotanni sun nuna cewa yaran sun nuna alamomin cutar irin su:
⚠️ Zazzaɓi mai tsanani
⚠️ Ciwon maƙogwaro
⚠️ Alamomin wahalar shaƙa
Bayan faruwar lamarin, jami’an lafiya sun kai ziyara gidan, inda suka tsaftace muhallin tare da yi wa sauran yara rigakafi a unguwar domin hana yaduwar cutar.
👉 Gwamnatin jihar Kano ta ce ta ware asibiti na musamman don kula da masu fama da mashaƙo, tare da tabbatar da cewa ana ba da rigakafi da magani kyauta ga yara.
Ta kuma yi kira ga iyaye da su tabbatar da yin rigakafin yaransu, da kuma gaggauta kai su asibiti idan aka fara samun alamomin cutar.