
Wasu ƴanbindiga da ake zargi ƴan Boko Haram ne sun yi garkuwa da fararen hula 11 da suke tafiya a wata motar bas a arewacin Kamaru.
Ƴanbindigar sun tare motar matafiyan ne a ranar 13 ga watan Agusta a tsakanin garin Zigague da Sale a arewacin Kamaru, lokacin da ƴanbindigar suka tare su, sannan suka yi awon gaba da su, kamar yadda kafar 237 online mai zaman kanta ta ruwaito a ranar 14 ga watan Agusta, inda rahoton ya ƙara da cewa motar na hanyar zuwa tsakanin Kousseri da Maroa ne.
“Ƴanbindigar sun saki macen da ke cikin matafiyan, amma suna ci gaba da riƙe da mazan,” kamar yadda rahoton ya nuna.
Wani kansila a yankin ya ce yana zargin akwai sa hannun masu kwarmata bayani a mutanen yankin, inda ya ce suna taka rawa wajen garkuwa da mutane.
“Maharan suna sane da zuwan motar,” in ji shi.
Yankin arewacin Kamaru na fama da matsaloli da dama na rashin tsaro irin su hare-haren Boko Haram da ambaliyar ruwa da ma talauci.