Jagoran ƙungiyar Hezbollah ya gargaɗi gwamnatin Lebanon kan cewa matsa wa ƙungiyar ta ajiye makamanta nan da ƙarshen shekara, zai iya jefa ƙasar cikin yaƙin basasa.
Naim Qassem ya ce shirin, wanda ya biyo bayan matsin lamba daga Amurka, kamar miƙa wa Isra’ila Lebanon ne.
Kafin yaƙin da aka yi tsakanin Hezbollah da Isra’ila a bara, ana hasashen ƙungiyar mai goyon bayan Iran na da makaman da suka fi na sojin Lebanon.
Duk da tsagaita wutar da aka yi a watan Nuwamba, Isra’ila ta ce za ta ci gaba da kai hari kan Hezbollah har sai ta ajiye makamanta baki ɗaya.