Yayin da ake ci gaba da tunkarar babban zaɓen 2027 a Najeriya, ƴansiyasa na ci gaba da lissafi da kitsa dabarun da za su kai su ga nasara.
Ƴansiyasa da dama na ci gaba da ƙoƙarin ƙulla ƙawance da zawarcin wasu, duk dai domin cimma babban burinsu na samun nasara a 2027.
A farkon makon nan aka samu wasu rahotanni da ke cewa ɓangaren tsohon shugaban ƙasa, GoodLuck Jonathan da ɓangaren Peter Obi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023 na tattaunawa a wani yunkuri na haɗuwa domin tunkarar zaɓen 2027.
A wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, a ƙarshen mako, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Dumebi Kachikwu ya yi iƙirarin cewa Jonathan ya yi wa Peter Obi tayin ba shi ministan kuɗi da tattalin arziki, idan ya jingine takara a zaɓe mai zuwa.