Gwamnatin jihar Neja ta amince da sulhun bayan fage a maimakon shiga kotu da gidan rediyon Badeggi (90.1 FM Radio Station) – kafar yaɗa labarai mai zaman kansa da ke garin Minna – wanda gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago, ya ba da umarnin rufewa.
Kafar yaɗa labaran ta shigar da gwamnatin jihar ƙara a gaban kotu kwanaki biyar bayan tilasta mata rufe gidan rediyon a ranar 5 ga Agusta ta hannun lauyanta mai suna, Philip Emmanuel.
A ranar Litinin, a lokacin zaman kotu kan shari’a mai lamba NSHCM/0296/2025 a gaban babbar kotun Minna mai lamba 4, inda lauyan gwamnati Jacob Usman ya sanar da cewa gwamnati tana son tattaunawa a wajen kotu domin sulhuntawa da gidan rediyon.
Usman ya bayyana wa kotun cewa ya tattauna da lauyan waɗanda suka shigar da ƙara domin warware matsalar saboda samun zaman lafiya albarkacin al’ummar jihar Neja.
Ya kuma bayyana wa kotun cewa ya riga ya sanar da mista Emmanuel cewa babban antoni-janar na jihar Neja ya amince ya warware matsalar a wajen kotu.
Mista Emmanuel daga baya ya tabbatar wa da ‘yan jarida cewa, “mun zaɓi ranar 3 ga Satumbar 2025 domin tattaunawa a wajen kotun.”
Mai shari’a, Mohammed Mohammed, a ranar 5 ga Agusta, ya amince da roƙon da mai shigar da ƙara gidan rediyon Badeggi Broadcasting Service Ltd, da manajin-daraktan Mohammed Badeggi.
A cikin hukuncin da ya yanke, mai shari’a Mohammed, ya dakatar da gwamnan jihar da antoni-janar da hukumar bunƙasa birane ta jihar daga ɗaukar mummunan mataki da ka iya shafar lasisin gidan rediyon da ginin gidan yaɗa labaran da ke harabar gidan NTA da ke saman dutsen Minna.
PREMIUM TIMES ta rawaito yadda gwamna Bago ya ba da umarnin rufe gidan rediyon Badeggi FM saboda zargin ƙoƙarin haifar da husuma.
Gwamnan ya ba da umarnin ne a lokacin zaman jiga-jigan jam’iyyar APC wanda aka yi a gidan gwamnati da ke Minna.
Ya kuma ce an ɗauki matakin ne saboda irin ayyukan da gidan rediyon ke yi wanda ya saɓa wa ƙa’ida.
Bago ya kuma zargi mamallakin gidan rediyon da ƙoƙarin tunzura al’umma a kan gwamnati inda ya buƙaci a soke lasisin gidan rediyon.
Gwamnan ya kuma ba wa kwamishinan tsaron cikin gida da rundunar ‘yan sanda umarnin rufe gidan rediyon.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama kamar SERAP da CJID sun yi Alla-wadai da matakin da gwamnan jihar ya ɗauka. Ƙungiyoyin sun kuma zargi gwamnan da ƙoƙarin murƙushe kafafen yaɗa labarai da tauye ‘yancin faɗar albarkacin baki a jihar.