Kamen nasa ya zo ne bayan rahoton nabban mai bincike na ƙasar, wanda ya zargi Maiga da lalata kayan gwamnati lokacin da yake mulki.
Tsohon firaministan ya bayyana a gaban hukumomi bayan sammacin da aka yi masa tare da sauran abokan aikinsa don yin bayani dangane da lamarin.
Masu nazari a ƙasar na ganin hakan a matsayin ci gaba da matsa wa ƴan adawa da gwamnatin mulkin ƙasar ke yi.