Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo jam’iyyar PDP, Malam Ibrahim Shekarau, ya jaddada cewa hadakar jam’iyyu kai tsaye ita ce hanyar kawar da gwamnatin Tinubu a 2027 ba ta ɗaiɗaikun mutane ba.
Shekaru ya ce ba a fahimci maganganunsa na baya ba kan haɗakar wasu ƴan siyasa a karkashin jam’iyyar ADC domin kwace mulki daga hannun APC.
Ya bukaci dukkan jam’iyyun adawa da su binciko hanyoyi da dabarun farfaɗo da dandalin siyasa domin cimma wannan buri, inda ya bayar da misalin yadda shi da wasu ƴan kishin ƙasa suka yi ƙoƙarin kafa haɗaka a 2011 domin kifar da tsohon shugaba Goodluck Jonathan daga mulki.