Fitaccen ɗan TikTok kuma mawaƙi a arewacin Najeriya, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da GFresh Al’amin ya ce shi ko kaɗan ba ya jin komai a irin yanayin yadda gudanar da harkokinsa a kafofin sadarwa, domin a cewarsa yana nishaɗantar da kansa, yana nishaɗantar da wasu, sannan kuma yana samun kuɗi.
Gfresh ya bayyana haka ne a zantawarsa da da shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, wanda ya zo tare da matarsa, Maryam Ahmad Yola.
A game da yadda ya fara samun ɗaukaka, mawaƙin ya ce da wahala ya fara harkokinsa har ya kai matakin da yake kai na ɗaukaka.
”Ni ne mawaƙin da yake waƙa ya haɗa kaset na CD ya bi tituna yana tallatawa. Dama can ina da masoya waƙoƙina, da TikTok ta fito kawai sai na ɗaura daga inda na tsaya, inda na cigaba da soki-burutsuna.”
Ya ce duk da cewa an fi ganinsa a TikTok a yanzu, ba ya daina waƙa ba ne, “amma kin san ni waƙar gambara nake yi, kuma salon waƙar bai karɓu sosai ba a arewacin Najeriya. Shi ya sa na ga ya dace yanayin ɗaukaka ta in riƙa yin abin da duk duniyar Hausawa yara da manya za su kalla ko su ji su samu nishaɗi, ba sai kananan yara ko matasa ba kawai. Shi ya sa na fara soki-burutsu, ina nishaɗantar da kaina, sannan ina nishaɗantar da miliyoyin mutane.”