Sanarwar korar ta fito daga Ofishin Sakataren yada Labaran Sakataren Gwamnatin Kano, Musa Tanko Muhammad.
Hakan ya biyo bayan Rahoton Kwamitin Bincike da Gwamna ya kafa kuma ya tabbatar wa da Kwamitin abubuwan da ake zarginsa.
An gano cewa Sharada, ya taka rawa da Kuma shirya yadda aka karɓi belin Sulaiman Danwawu da ake zargi da dillancin miyagun kwayoyi.
Gwamnati ta gargade shi da kada ya kuskura ya sake bayanna kansa a matsayin Jami’in Gwamnatin Abba Kabir Yusuf mai ci a yanzu.