Wani soja wanda ba a daɗe da yaye su ba, Dauda Dedan, ya yi layar zana bayan zargin sa da kashe wani ɗansanda, Aaron John, ta hanyar canja masa wuƙa a Jalingon jihar Taraba.
A yayin da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, James Lashen, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9. na dare a Mayo-Goyi, da ke wajen garin Jalingo.
Lashen ya ce, ɗan sandan ya samu rashin fahimta ne da wasu mazauna yankin da wannan soja ya soka masa wuƙar.
Kakakin rundunar wanda ya ƙara da cewa an nemi sojan an rasa a yayin da rundunar tasu ta tabbatar da cewa tana bincike kan lamarin kuma ta ba wa rundunar ‘yan sanda tabbacin bin diddiginsa domin kama shi da hukunta shi.
“Mun shigar da rahoto kan lamarin a runduna ta 6 ta sojin Najeriya kuma an ba mu tabbacin bindiddiginsa da kama shi domin ya girbi abin da ya shuka.
“Rundunar ƴan sanda da ta soja suna aiki tare. Mu je gidan da sojan ke zaune. Za mu tabbata mun kama shi tare da hukunta shi daidai da abin da ya aikata,” ya faɗa.
Lashen ya ce, babu wani tashin hankali tsakanin rundunar sojin da ta ‘yan sanda. Alaƙarsu na nan kamar yadda aka saba.
Wani soja wanda ba a daɗe da yaye su ba, Dauda Dedan, ya yi layar zana bayan zargin sa da kashe wani ɗansanda, Aaron John, ta hanyar canja masa wuƙa a Jalingon jihar Taraba.